Connect with us

Labaran Najeriya

Obasanjo ya bayyana yadda Ya Tsira daga hadarin Jirgin Sama a ranar Laraba da ta wuce

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Tsohon Shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya gabatar da irin yanayin da shi da wasu mutane suka iske kansu a lokacin jirgin sama ya tashi kihewa da su a ranar Laraba 29 ga watan Mayu da ta gabata.

Ka tuna da cewa ranar Labara, 29 ga Mayu ne aka yi hidimar rantsar da shugaba Muhammadu Buhari a shugabancin Najeriya a karo ta biyu ga mulkin farar hula.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa hadarin jirgin saman ya tashi faruwa da Obasanjo ne a yayin da suke bakin sauka daga kan tafiya a Filin Jirgin Sama da Murtala Muhammed da ke a birnin Legas.

Jirgin saman mai lamba Boeing 777-300, ya tashi kihewa ne da mutane a kalla dari hudu (400), hade da Obasanjo, a ranar Laraba.

A bayanin Obasanjo da manema labaran PREMIUM TIMES, ya fada da cewa ”Na kasance da hankali na kwance ina karatun jarida na a yayin da jirgin ke kokarin kihewa da mu” inji shi.

“A lokacin da abin ke faruwa, Na kafa ido da karatun jarida na, Da wani mutumi da ke gefe na ya gane da hakan sai ya tuntube ni da tambaya. Shin Oga ba zaka nuna damuwa bane? inji mutumin, Sai na amsa masa nace, Shin idan na damu sai me? Zan iya dakatar da jirgin daga kihewa da mu ne?”

Shin idan ka iske kanka cikin irin wannan yanayi, me zaka iya yi? Obasanjo na tambaya.

“Kawai ni na barwa komai ga Allah ne, tunda ba abinda zai iya yi ga al’amarin” inji shi.

Naija News Hausa na da sanin cewa Obasanjo hakan ya faru ne da tsohon shugaban a lokacin da suke dawowa daga wata taron masu ruwa da tsaki na kasar Afrika, da suka kamala ranar Talata da ta wuce a birnin Addis Ababa.

An bayyana da cewa jirgin ya tashi kifewa ne sakamakon wata goguwa mai karfin gaske a yayin da suke kan sauka.

Amma abin godiya, jirgin ta sauya daga hakan, ta lake a kan iska da  tsawon mintoci goma tsaye kamin ta iya sauka bayan lafawar goguwar.

KARANTA WANNAN KUMA: Akalla Mutane 7 suka mutu a karon Motar Dangote da wata Motar Bas a hanyar Jos