Connect with us

Uncategorized

‘Yan Hari da Bindiga sun kashe akalla mutane 16 a Ranar Sallar Eid-Al-Fitr a Zamfara

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Naija News Hausa ta karbi rahoto da cewa mahara da bindiga sun kashe akalla mutane 16 a ranar Salla, a yankin Bakoma ta karamar hukumar Maru da ke a Jihar Zamfara.

Don bada tabbaci ga lamarin, Daraktan sadarwa ga Gwamnan Jihar Zamfara, Yusuf Idris ya bayyana ga manema labarai a Gusau ranar Laraba da ta wuce da cewa lallai hakan ya faru kuma gwamnan Jihar ya ziyarci yankin don gaisuwar musanman da ta’aziya ga iyalin mutanen da aka kashe.

“A ziyarar gwamnan a yankin, ya umarci hukumomin tsaro da daukan matakin musanman don tabbatar da kame mutanen da suka aiwatar da mugun harin”

Ya kara cewa Gwamnan ya dauki nauyin daukar mutane 14 da aka yiwa rauni da harsasun bindiga daga asibitin Kanoma General Hospital zuwa babban Asibitin Tarayya ta Federal Medical Centre, Gusau, don basu kulawa ta musanman.

“Jihar zata dauki nauyin kudaden da za a kashe a kan su don basu isashen kulawa” inji shi.

Wakilin kauyan Kanoma, Yahaya Mohammed ya bayyana ga gwamnan da cewa, “mahara da bindigar sun fada wa kauyen ne da maraice da harbe-harben bindiga har ga kashe mutane 16, da kuma yiwa mutane 14 rauni da harbi”