Uncategorized
An Kashe akalla mutane 18 a wata sabuwar harin ‘yan ta’adda a Jihar Sokoto
A daren ranar Asabar da ta gabata, Mahara da Bindiga sun kashe akalla mutane 18 a kauyukan da ke a karamar hukumar Rabah, Jihar Sakwato.
Harin ya bar mutane da kirgan raunuka daban daban, a yayin harbe-harben harsasu a sama da mahara suka yi.
Naija News Hausa ta samu tabbacin rahoton ne bisa sanarwan da Ciyaman na Zakkat da kuma shugaban Kwamitin Jiha ga ragaggu mutane (IDPs), Malam Lawal Maidoki ya bayar ga manema labarai ranar Lahadin da ta gabata.
An bayyana kuma da cewa Ciyaman din da sauran hukumomin tsaron Jihar sun ziyarci kauyan Rakumni, Tsage da kuma Kalgo don ceton rayuka da kuma ta’aziya, anan kazalika suka tattara gawakin mutanen da aka kashe don shirya su ga hidimar bizinewa.
Ko da shike ba a samu karban bayani ba daga bakin DSP Sadik Abubakar, kakakin yada yawun Jami’an tsaron Jihar Sokoto ba a lokacin da aka bayar da wannan rahoton.
KARANTA WANNAN KUMA; Kalli yadda mazauna suka yiwa wani barawo da aka kame a Jihar Niger Delta