Connect with us

Uncategorized

Kalli yadda aka yiwa wani barawo da aka kama a Niger Delta

Published

on

Wani matashi, barawo ya kai ga karshen sata a yayin da ya fada a hannu mazuana bayan da yayi kokarin sace babur a Niger Delta.

An kama barawon ne da ake zargi da zama daya daga cikin mugan barayi da ke satar baburar mutane a Jihar Rivers. Rahotannai sun bayar cewa an kame matashin ne a shiyar Alesa da ke a yankin Eleme, nan Jihar Rivers da safiyar yau Jumma’a, aka kuma yi mashi dukar tsiya, kamar a kashe shi.

Bisa sanarwa da Naija News Hausa ta gane da shi, barawon ya sace wata babur ne da ake kira ‘ladies machine’ a nan shiyar Alesa, da aka gane da hakan kuma sai aka bi shi da gudun tsiya a yayin da yake kokarin guduwa da baburar.

Ka tuna mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Rundunar Sojojin Najeriya sun dakatar da amfani da bubura a wasu Jihohin Najeriya, akan matsalar ta’addanci da sace-sace da ake fuskanta a jihohin.

Mazauna garin Alesa ta Jihar Rivers sun ci nasara da kame barawon ne bayan da Man Fetur ta kare a cikin babur da barawon yake batun guduwa da ita, “kwaram sai ya fada a cikin daji da kokarin boye mashin din. A garin hakan ne aka ci karo da shi, anan aka fara yi masa mugun duka” inji mai bada labarai.

Kalli hoton barawon a kasa;