Connect with us

Labaran Najeriya

Lawan: Omo-Agege ya lashe zaben Mataimakin Shugaban Sanatocin Najeriya

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Dan takaran kujerar mataimakin shugaban Sanatocin Najeriya, Ovie Omo-Agege ya lashe tseren zaben da aka yi a yau Talata, 11 ga watan Yuni 2019.

Ka tuna mun sanar a baya da cewa Ahmed Lawan ya lashe zaben kujerar shugabancin gidan Majalisar Dattijai da kuri’u 79, fiye da dan adawan sa daga Jam’iyya PDP, Ali Ndume, mai yawar kuri’u 28.

Bayan da aka gabatar da Omo-Agege a matsayin mai nasara ga zaben mataimakin shugaban Majalisar, shugabancin zaben ta rantsar da sabbin ‘yan Majalisa na 9 tare da shugaban gidan Majalisar, Ahmed Lawan da mataimakin sa Ovie Omo-Agege.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Kotu ta gabatar da sabon Alkali da zai wakilci Kotun Neman yancin zabe akan karar zaben shugaban kasa ta watan Fabrairu, tsakanin shugaba Muhammadu Buhari da Alhaji Atiku Abubakar.

Alkali M. L Garba, zai maye gurbin tsohon jagoran Kotun, Bulkachuwa a hidimar karar zaben shugaban kasa ne bayan da Jam’iyyar PDP da manya a kasar suka bayyana rashin amincewa da Bulkachuwa da kasancewa a shari’a Kotun, da zargin cewa tana da alaka da Jam’iyyar APC.