Connect with us

Uncategorized

‘Yan Majalisar Dokoki 6 a Jihar Imo sun koma ga Jam’iyyar PDP

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Rahoto ta bayar a ranar Litini da ta gabata da cewa ‘yan Majalisar Dokoki shidda a Jihar Imo sun yi murabus da Jam’iyyar su, sun koma Jam’iyyar Adama (PDP).

‘Yan Majalisar sun gabatar ne da komawarsu ga Jam’iyyar PDP a wata wasika da suka wallafa, wadda aka karanta a bakin magatakardan gidan majalisar jihar, ranar Litini da ta wuce.

An bayyana da cewa biyar daga cikin ‘yan majalisar sun yi murabus ne da tsohon majalisar su, Action Alliance (AA), na shiddan kuma dan majalisar All Progressives Grand Alliance (APGA) ne.

Ga sunayan su kamar haka da kuma tsohon jam’iyyar su;

Suna                                      Yanki                            Tsohon Jam’iyya

Mike Iheanaetu       –          Aboh Mbaise       –      AA

Victor Onyewuchi   –          Owerri West        –      AA

Ken Agbim               –          Ahiazu Mbaise     –     AA

Lloyd Chukwuemeka         Owerri North       –     AA

Bruno Ukoha                       Ezinihittte Mbaise     AA

Chiji Collins                         Isiala Mbano              APGA

Ko da shike an iya gane da cewa Mista Collins yayi murabus da Jam’iyyar APGA ne don samun daman zama shugaban Majalisar Jihar a nan gaba.

KARANTA WANNAN KUMA; Ku bamu Takardan Yancin Jagorancin Mu, Sanata a PDP na Jihar Bauchi da Mamba 4 sun kalubalanci Hukumar INEC.