Uncategorized
‘Yan Hari da Bindiga sun sace Wakilin Garin Labo a Jihar Katsina
Naija News Hausa ta karbi rahoto da cewa wasu mahara da makami da ba a gane da su ba sun sace, a ranar Talata 11 ga watan Yuni, da tsakar ranar sun sace Wakilin Garin Labo da ke a karamar hukumar Batsari, a nan Jihar Katsina.
Ko da shike ba a bayyana sunan sarkin kauyan ba, amma bisa rahoton da aka bayar a layin yanar gizo ga Naija News, an sace wakilin ne da tsakar ranar Talata a missalin karfe 1pm, a yayin da yake kan aiki a gonarsa tare da wasu mazauna a kauyan.
Masu bada labarai sun bayyana da cewa ‘yan hari da makamin sun fada a gonar wakilin ne a saman baburori da suka tafo da su, suka kuma fara harbe harbe a iska.
“Maharan sun sace wakilin ne a yayin da yake aiki a gonarsa tare da mazauna a kauye. Sun ci nasara da hakan ne bayan da suka haro gonar a saman babur da harbe harbe don tsorata mutane, da kuma kowa ya gudu sai suka sace sarkin” inji mai bada labari ga manema labarai.
Kakakin yada yawun hukumar Jami’an tsaron Jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya bada tabbacin hakan a wata sanarwa da aka bayar ranar Laraba da ya gabata.
“Tabbas harin da gaske ne. Ko da shike rukunin tsaro ta Operation Puff Adder sun yi gwagwarmaya da gano ‘yan harin, amma da yake an sace wakilin ne a gonar sa da ke kusa da dogon dajin Rugu, ba a samu nasara da kame su ba don maharan sun fada dashi a cikin dogon dajin Rugu kamin isowar jami’an tsaro” inji Isah.
Ya karshe da cewa hukumar na kan bincike da hakan, da kuma yin kira ga al’umma da sanar da duk wata alama ko liki da zai taimaka wajen kama ‘yan ta’addan.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Hukumar Tsaro sun kame wani mutum mai taimakawa Boko Haram da kayan hada Bama-bamai a shiyar Maiduguri, Jihar Borno.