Connect with us

Uncategorized

Jirgin Rundunar Sojojin Sama ya rushe a Jihar Katsina a yayin sauka

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Daya daga cikin Jirgin sama da Rundunar Sojojin Sama ke yawo da ita a Jihar Katsina ya rushe a yayin da suke kokarin sauka.

An bayyana hakan ne ga Naija News Hausa a wata sanarwa da aka bayar ranar Laraba da ta wuce, daga bakin mista Ibikunle Daramola, Daraktan yadar da labarai ga rundunar.

Abin ya faru ne a yayin da Jirgin ke kokarin saukar da Sojoji a Filin Jirgin sama ta Umaru Musa Yar’adua International Airport, Jihar Katsina.

Bisa bayanin Mista Daramola, Jirgin ta fashe ne da darukan Sojojin Operation Hadaran Daji a missalin karfe Uku na rana Laraba da ta wuce, a yayin da suke dawowa daga wata hari a Arewacin Najeriya.

Ko da shike har yanzu ba cikakken bayani game da hadarin, amma kakakin yada yawun sojojin ya bayar da cewa babu wanda ya mutu a hadarin.

KARANTA WANNAN KUMA; Bayanin sabon Shugaban Gidan Majalisar Dattijai, Ahmed Lawan bayan nasara da zabe.