Uncategorized
Kannywood: Kalli Inda zaka iya ta samun Sabo Fina-Finan Hausa a ko yaushe
Kamar yada muka sanar a shafin labaran mu a baya da cewa ana shirin fara haska Fina-Finan Hausa a shafin NorthFlix Media, tau jita-jita ya kare, NorthFlix ya fara aiki.
Kamar yadda ka aza Whatsapp da Facebook a wayar Salula da kake amfani da ita, haka kazalika kana iya aza Manhajar @northflixng a wayar ka na #Android domin more wa kallon sabin Fina-Finan Hausa.
An sanar da wannan ne a layin yanar gizon nishadarwa ta Twitter. Kana iya shiga Manhajar GooglePlay da ke a wayar #Android naka don samun Manhajar NorthFlix.
Kalli sanarwan kamar yadda aka bayar a Kannywood;
Ku sauke manhajar @northflixng a wayoyinku na #Android domin more kallon finafinan Hausa.
Hajiya @AdizatouGabon Northflix na godiya. pic.twitter.com/wFJgEe1U55
— Northflix Media (@NorthflixMedia) June 17, 2019