Connect with us

Uncategorized

An katange Makarantan Jami’ar Fasaha ta Rufus Giwa da shiga Yajin Aiki

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Mallaman Makarantar Fasaha ta Rufus Giwa (Polytechnic) da ke a Owo, Jihar Ondo, a yau sun kafa kai ga yajin aiki mara ranar karshewa.

Naija News Hausa ta gane a rahotannai da cewa Mallaman sun shiga yajin aikin ne don rashin biyan su Albashi na tsawon watannai.

Ko da shike a wata sanarwa da Rajistan makarantar, Mista Sule Atiku ya bayar, bai bayyana dalilin yajin aikin ba, amma rahotannai sun bayyana da cewa hakan ya faru ne akan matsalar da ke a tsakanin hukumar kadamarwa na makarantar da Kungiyar Mallaman Jami’a ta Fasaha.

Gidan Talabijin yada Labarai ta TVC ta sanar da cewa Malamai da Ma’aikatan Makarantar sun shiga yajin aiki ne don rashin biyan su albashi da kuma bayar da wasu ababe da ya dace da su a tsawon watannai.

A hakan ne aka sanar da gargadin daliban makarantar, Maza da Mata da barin ciki da kewayen makarantar kamin karfe 3 na ranar yau.