Uncategorized
NAFDAC ta bada Umurnin hana sayar da Sniper a kasuwa don magance yada ake amfani da shi ga Kisan Kai
Hukumar Kula da harkokin Abinci da magunguna ta tarayyar Najeriya (NAFDAC), sun bada umurni ga masu sayar da magungunan aikin feshin gona da lambu da su janye daga sayar da mugun maganin da aka fi sani da SNIPER, da ake amfani da shi wajen kashin kwari.
Hukumar ta umarci masu sayar da Sniper da barin saye da sayar da shi a dukan kasuwar Najeriya, danin irin yadda yawar mutane ke karuwa wajen amfani da mugun maganin don kisan kai.
Naija News Hausa ta gane da sanarwan ne bisa yadda hukumar ta sanar daga bakin Daraktan hukumar NAFDAC ta Cibiyar Nazarin Kwayoyin Dabbobi da Gonaki, Dokta Bukar Usman, a Cibiyar Nazarin Noma ta Tarayyar kasa (IITA) da aka yi a birnin Ibadan, ranar Laraba, 19 ga Yuni da ta gabata, kamar yadda jaridan Leadership suka sanar..
Mista Usman, a yayin da yake cikin jawabin sa a taron, ya fada da cewa “Maganin Sniper ba maganin da ya kamata ana sayarwa don aikin gona ba. An tsarafa maganin ne don aikin gona amma ba don amfanin gida ba”
Ya kuwa gargadi diloli da kuma bukatarsu da bada hadin kai ga hukumar NAFDAC don tabbatar da cin nasara ga magance amfani da maganin a gidaje.
“Ba wai za a hana sayar da shi ko fid da shi daga kasuwa bane. Amma za a hana sayar da shi a kasuwa da shagogi don amfanin gida, don magance matsalar yadda aka amfani da shi waje kashi da kisan kai” inji Mista Usman.
Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Wani dan Shekara 12 a Jihar Kogi ya sha Gamale don kisan kansa.
Yaron da aka gane da suna Bobo, ya sha maganin kashe kwarin ne bayan da yayar sa ta tsawata masa akan wata laifi da yayi.