Connect with us

Labaran Najeriya

‘Yan Harin da Bindiga sun saki Surukin Shugaba Muhammadu Buhari da aka sace a baya

Published

on

at

Listen to article
00:00 / 00:00

Surukin Shugaba Muhammadu Buhari da ‘yan hari da makami suka sace a baya ya sami yanci a yau

Naija News Hausa ta karbi rahoto bisa bayanin dan uwa ga Alhaji Musa Umar Uba, da cewa ‘yan hari da makami sun sace Magajin Garin Daura da aka sace a baya a Jihar Kano.

“Ina baku tabbaci da cewa a halin yanzu an riga an saki Magajin Gari, yana kuma cikin koshin Lafiya a nan Kano. Mun kuwa gode ga Allah” inji bayanin kani ga Magajin Daura, Malam Umar Umar Ata (Dan Lawan Daura), a bayanin sa da manema labaran Daily Trust.

Naija News ta fahimta da cewa an saki Umar Uba ne bayan tsawon watannai biyu da aka sace shi”

Haka kazakila kakakin yada yawun Jami’an tsaron Jihar Katsina, SP Gambo Isah ya bayar da tabbacin hakan a wata sako da ya aika wa manema labarai.

Sakon na kamar haka;

“Magajin Garin Daura ya sami yanci fita daga kangin ‘yan hari da makami. Muna isar da murna ga Iyalan sa da kuma dukan al’umar garin Daura da Jihar Katsina”

Ko da shike bisa rahoton Kungiyar manema labaran Najeriya (NAN), sun bayyana da cewa an ci nasara da karban yancin Magajin Daura ne a taimako da kuma hadin kan hukumomin tsaron Jihar, a wata ganawar wuta da suka yi da ‘yan ta’adda da suka sace shi.

Anyi ganawar wutan ne a shiyar babban hanyar Madobi, Samagu quarters, kusa da Gidan Matasa na Sani Abacha (Sani Abacha Youth Center) da ke a Kano.

KARANTA WANNAN KUMA; Jami’an Tsaro sun kame wani Soja mai sayar da Makami ga ‘Yan Fashi