Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba, 3 ga Watan Yuli, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba, 3 ga Watan Yuli, 2019

1. Al’umar Najeriya sun riga sun yada yawunsu, mu kuma ba zamu kunyatar da su ba – Buhari

A ranar Talata da ta gabata, shugaba Muhammadu Buhari, a birnin Abuja ya fada da cewa sakamakon zaben 2019 ya bayyana bukata da zabin al’umar kasar Najeriya, ya kuwa buga gaba da cewa ba zai kunyatar da al’umar kasar ba a shugabancin sa ta karo na biyu.

Shugaba Buhari ya fadi hakan ne a hidimar Buhari Support Group Centre, wadda Alhaji Umaru Dembo ya jagoranta a Majalisar Jiha.

2. Shugaban Sanatocin Najeriya, Lawan ya gabatar da Manyan jagora a Majalisar Dokoki na 9

Shugaban Sanatocin Najeriya, Ahmed Lawan a ranar Talata da ta wuce ya sanar da sunayan Jigo da masu jagora takwas a majalisar Dokoki na tara.

Wannan matakin ya biyo ne bayan wata wasika da aka bayar ga Lawan daga hannun Ciyaman na Tarayyar Jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole da Ciyaman na Jam’iyyar Dimokradiyya (PDP), Uche Secondus.

3. Atiku ya bayyana matakin da zai dauka akan EFCC da zargin Saraki

Tsohon shugaban kasan Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya mayar da martani ga matsalar da ke a tsakanin Hukumar EFCC da tsohon shugaban sanatocin Najeriya a Majalisa na takwas, Dakta Bukola Saraki.

“Akwai banbanci tsakanin la’antarwa da cin zalunci” inji Atiku a wata sako da aka bayar ga Naija News a ranar Talata da ta wuce.

4. Buhari bai aika jerin sunan Ministoci ba tukuna – inji shugabanci

Shugabancin kasar Najeriya ta karyace rahoton da aka bayar a layin yanar gizo da cewa shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata da ta wuce ya bayar da jerin Ministoci da zasu kasance a rukunin shugabancin sa ga ‘yan Majalisar Dokoki.

Haka kazalika Mallam Shehu ya ya karyace cewa ya bada tabbacin hakan a layin yanar gizo.

5. Kotu ta yantar da Fayose, an kuma bashi daman tafiya zuwa kasar Turai

Hukumar Kare Tattalin Arzikin kasa da yaki da Cin Hanci da Rashawa a Najeriya ta sake gabatar da tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose a gaban Kotun Kolin Tarayya da ke a Jihar Legas, a jagorancin Alkali Chukwujekwu Aneke

Naija News ta fahimta da cewa an gabatar da tsohon Gwamnan da kuma jigo a Jam’iyyar PDP ne a Kotu tun ranar 22 ga Aktoba da ta gabata a gaban Kotu da zargin 11 akan boye kudi Nairan Biliyan N1.2b da kuma sace Dala Miliyan $5m daga asusun Ofishin National Security Adviser (ONSA).

6. Asusun Jihar Oyo na a fanko ne – Makinde

Sabon Gwamnan Jihar Oyo, Mista Seyi Makinde ya bayyana da cewa gwamnatin jihar ta da duk ta mayar da asusun jihar a fanko.

A bayanin Gwamna Seyi, ya fada da cewa gwamnatin sa har yanzu tana gwagwarmaya da neman yadda za ta kadamar da ayuka a jihar da irin mumunar yanayi da asusun jihar ke da shi.

7. Mahara da Bindiga sun saki Surukin Buhari

Surukin shugaba Muhammadu Buhari, Mallam Musa Umar ya samu yanci daga hannun ‘yan hari da bindiga da suka sace shi tun kwanakin baya da suka shige.

Naija News Hausa ta tuna da cewa an sace Magajin Garin Daura ne tun ranar Laraba, 1 ga watan Mayu, 2019 da ta gabata a nan fadar sa da ke a Daura, Jihar Katsina.

8. Gobarar wuta ya ratsa Gidan Radiyon da ke a Bayelsa

A ranar Talata da ta wuce, wata mumunar Gobarar wuta ya kone Gidan Radiyon da Jihar Bayelsa ke da ita.

Naija News ta fahimta da cewa gobarar wutan ya kone wata shiya ne mai muhinmacin a gidan Radiyon da ke a hanyar Azikoro, Yenagoa babban birnin Jihar Bayelsa.

Ka sami kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com