Uncategorized
AFCON: ‘Yan Wasan Kwallon Kafan Najeriya, Super Eagles nada wasa yau, kali lokaci
A yau Laraba, 10 ga watan Yuli 2019, ‘yan wasan kwallon kafa ta Najeriya da aka fi sani da ‘Super Eagles’ zasu gana a yau da ‘yan wasan kwallon kafan kasar South Africa da ake kira da suna ‘Bafana Bafana’.
Wasan kwata Final din da ke da alamar zafi za a yi shi a misalin karfe takwas (8:00 PM) na daren yau Laraba a filin wasan kwallon Cairo a kasar Egypt.
Ka tuna da cewa ‘yan wasan Super Eagles, a ranar Asabar da ta gabata sun lasa ragar ‘yan wasan kwallon kafan kasar Kamaru da gwalagwalai 2 ba ko daya.
Ko da shike, bisa ganewar Naija News Hausa, jigon ‘yan wasan kafar Najeriya da kuma Kaftin ga Super Eagles, Mikel Obi ba zai samu buga wasar ba saboda rauni da yake da ita.
KARANTA WANNAN KUMA; ‘Yan Hisbah sun kame mutane 48 da kuma kwace katan kayan maye 37 a Jigawa.