Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis, 11 ga Watan Yuli, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis, 11 ga Watan Yuli, 2019

1. Shugaba Buhari zai bayar da jerin Ministoci ga Majalisa a wannan makon

Ko da wata canjin ra’ayi ko jinkirta, shugaba Muhammadu Buhari a wannan makon zai bayar da jerin sunayan ministoci da zasu yi jagoranci a rukunin shugabancin sa ta karo biyu ga Majalisar Dokokin Najeriya.

Naija News Hausa ta gane da hakan ne a sanarwan shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Ahmad Lawan ya bayar a birnin Abuja ranar Laraba da ta wuce.

2. Najeriya na cikin tulin bashi na naira N25trillion  – DMO

Hukumar Kula da Bashin kasa, da ake kira da ‘Debt Management Office (DMO) ta gabatar da cewa Gwamnatin Tarayyar Najeriya, Gwamnatin Jiha da birnin Tarayya (FCT) na cikin dungun bashi na naira Tiriliyan ₦24.947tr.

Naija News ta fahimta da hakan ne a wata sanarwa da aka bayar ranar Laraba da ta gabata.

3. Bari mu janye karar zargin mu ga Buhari – inji Jam’iyar PDM

Ciyaman Tarayyar Jam’iyyar Peoples Democratic Movement (PDM), Mista Frank Igwebuike ya isa ga hukumar Kotun kara da ke jagorancin karar zaben shugaban kasar Najeriya, da bukatar janye karar da suka gabatar akan nasarar shugaba Muhammadu Buhari.

Bayan karban bayanin, Alkali Mohammed Garba ya gabatar da ranar 8 ga watan Yuli don karban cikakken bayani game da zancen.

4. Atiku ya zargi shugabancin Buhari da yawar bashi

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar ya kalubalanci gwamnatin shugaba Muhammadu Buahri da cika da yawar bashi.

Naija News ta gane da cewa Atiku ya fadi hakan ne da ya gane da zancen bashin tiriliyan ₦24.947trn da kasar ta ci a sanarwan hukumar DMO.

5. NJC sun gayawa Buhari wanda ya dace da ya sanya a matsayin sabon CJN

Kungiyar Tarayyar Alkalan Najeriya (NJC), a ranar Laraba da ta wuce sun gargadi shugaba Muhammadu Buhari da sanya Alkali Ibrahim Tanko Muhammad a matsayin babban alkalin kasar Najeriya (CJN).

NJC sun gabatar da hakan ne a bakin Soji Oye, kakakin yada yawun hukumar a wata ganawa da suka yi a ranar Alhamis, 11 ga watan Yuli.

6. Ku bar Adeboye, ku kalubalanci Buhari – CAN ta gayawa masu zanga zanga

Hadaddiyar Kungiyar Kiristocin Najeriya, CAN ta gargadi wadanda suka fita zanga-zanga da bukatar cewa Fasto Enoch Adeboye, babban faston Ikilisiyar The Redeemed Christian Church of God (RCCG) ya kafa baki ga zancen RUGA.

Wannan bayanin CAN ya biyo ne bayan da sananan mawakin Najeriya, Eedris Abdulkareem, hade da Baba Fryo, Felix Duke da Charley Boy suka fita zanga zanga da ikirarin sunan Adeboye da yin bayani game da zancen kafa RUGA.

7. Super Eagles sun lashe ragar Bafana Bafana

‘Yan wasan kwallon kafan Najeriya da ake kira da ‘Super Eagles’ sun lashe ragar ‘yan wasan kwallon South Africa da ake kira Bafana Bafana, da gwalagwalai 2 da 1 a wasar su ta ranar jiya Laraba.

Wannan nasarar ya kai su ka shiga tseren Semi-Final, wata karo ta karshe ga shiga Final.

8. An sace Sakataren Adamawa a wata munsayar harsasu da mahara

An sace Babban Magatakardan Jihar Adamawa, Emmanuel Piridimso, a wata munsayar harsasu da ‘yan fashi, ranar Laraba da ta wuce.

Naija News Hausa ta fahimta ne da cewa an sace Mista Emmanuel ne a gidansa da ke a Yola, babban birnin Jihar Adamawa.

Ka samu kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com