Connect with us

Uncategorized

‘Yan Sanda sun kame mutane 37 da laifuka a Jihar Katsina

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Rukunin Hukumar ‘Yan Sandan Jihar Katsina, ta sanar da kame wasu mutane 37 a Katsina da ake zargin zama ‘yan ta’adda, a ranar Talata da ta gabata.

Naija News Hausa ta gane da hakan ne a wata sanarwa da Kwamishanan Hukumar Tsaron, CP Sanusi Buba ya bayar ga manema labarai a hedikwatan Jihar ‘yan sandan da ke a Katsina.

Sanusi ya bayyana ga manema labarai da cewa jami’an tsaron su ta kama mutanen ne da laifuka kamar sace mutane, fashi da makami, sace-sace dabobi da kuma hari da bindiga.

A bayanin sa ya iya bada haske da cewa an kamu mutanen ne a yankuna daban daban. Wasu daga yankin Sabuwa, Dandume dadai sauran su.

Kalli ire-iren miyagun makamai da aka ribato daga hannun mutanen da aka kama;

Bindigar AK49 guda 14, Rifles guda (3), Pump Action bakwai (7), Adduna tara (9) da wasu miyagun bindigogin Turai da ta kirar bakar fata daban daban.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da Rundunar Sojojin Najeriya sun ribato rayuka 13 daga ‘Yan Hari da bindiga