Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba, 17 ga Watan Yuli, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba, 17 ga Watan Yuli, 2019

1. Tsohon Shugaban kasar Najeriya, Goodluck ya kalubalanci Gwamnatin Buhari

Shugaban Najeriya na da, Goodluck Ebele Jonathan, ya kalubalanci shugabancin APC a jagoranci gwamnatin tarayya a kan karuwa ga yawan rashin tsaro a kasar.

Naija News ta fahimta da cewa tsohon shugaban ya bayyana da cewa kasar na yawaita kullum da matsaloli.

2. Majalisar Dattijai ta Nijeriya ta gabatar da Babban Taron Tsaron kasa

A ganin irin mumunar hare-hare da ake kai ga al’umar Najeriya, Majalisar Dattijai ta Nijeriya ta yi kira ga taron gaggawa na Kwamitin Tsaron kasa.

An gabatar da zancen taron ne a bakin Shugaban Majalisar Dattijai, Ahmed Lawan, bayan wata zance da Sanata Ayo Akinyelure ya gabatar a kan kisan da aka yi wa Mrs Funke Olakurin, diyar shugaban Afenifere.

3. Kwamitin NLC tayi barazanar yin Yajin Aiki

Shugaban Kwamitin Jakadancin Najeriya (NLC), Comrade Ayuba Wabba ya bayyana cewa majalisar ba ta bayar da wata sanarwa ba ga shiga yajin aiki akan jinkirtan Gwamnatin taraya bisa biyan kankanin albashin ma’aikata.

Bisa ganewar Naija News Hausa, Wabba ya nuna cewa hukumar na kan tattaunawar akan aiwatar da mafi kankanin albashin ma’aikatan kasa.

4. Ba Kada manufa ta kwarai akan Najeriya, Buhari ya gayawa Obasanjo

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya bayyana da cewa wadanda ke dogara ga matsalolin rashin tsaro a kasar don tayar da farmaki ko wata zance mara dadi basu cika ga manufan kwarai ga kasar ba.

Shugaban ya fadi hakan ne a lokacin da ya karbi ziyarar shugabanni na hukumar neman zaben sa (BCO), anan fadar  shugaban kasa, Aso Rock.

5. Mai bada Shaida ga PDP ya zargi malaman zabe da karban cin hanci na dala $10,000

Wani mai shaida ga jam’iyyar PDP akan hidimar karar zaben shugaban kasa, Peter Ali, a yayin da yake jawabi a kotun koli na kasa a ranar Laraba, ya zargi wani jami’in hukumar zabe mai suna Abubakar Kaura da karban cin hanci da rashawa na dala 10,000 a ranar zaben.

Ali, wanda ya yi ikirarin cewa shi jami’in zabe ne a wata mazaba ya bayyana cewa dala dubu 10,000 ne aka bayar ga malamin zaben, Abubakar, don kadamar da makirci a sakamakon zabe a yankin Nasarawa.

6. Majalisar Dattijai ta shirya da binciken CJN Tanko Mohammad

Majalisar Dattijai ta Nijeriya ta yi alwashin binciken alkalin kotun Najeriya, Tanko Mohammad a ranar Laraba (Yau).

Ka tuna da cewa shugaba Muhammadu Buhari, a makon da ta gabata bada sunan alkali Tanko Tanko ga Majalisar Dattijai don tabbatarwa ga matsayin shugaban alkalan kasar.

7. Kotun Koli ta Bayyana hukunci ga karar Mista Ned Nwoko

Kotun Koli a ranar talata da ta wuce tayi watsi da karar da Ned Nwoko ya gabatar akan kalubalantar zaben Sanata Peter Nwaoboshi a matsayin dan takaran PDP mai wakiltar yankin Arewacin Delta.

Naija News ta fahimta ne da cewa Nwoko na kalubalantar nasarar Peter ne a zaben firamare da aka yi a ranar 2 ga Oktoba, a shekarar 2018, wanda aka bayyana Peter a matsayin mai nasara ga matsayin dan takarar PDP.

8. Ku kama Obasanjo Yanzu, Miyetti Allah ta gaya wa Gwamnatin Tarayya

‘Yan Kungiyar Miyetti Allah (MACBAN) sun bukaci gwamnatin tarayyar Najeriya da kama tsohon shugaban kasar, Olusegun Obasanjo.

Kungiyar ta bayyana hakan ne bayan wata wasika da tsohon shugaban ya wallafa da kuma aika wa shugaba Muhammadu Buhari a ranar 15 ga Yulin game da abubuwan da ke faruwa a kasar, da kuma matsalar tsaro da ake fuskanta.

Ka samu kari da cikakken Labaran Najeriya a Naija News Hausa