Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 6 ga Watan Agusta, Shekara ta 2019

Published

on

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 6 ga Watan Agusta, 2019

1. Kotu Ta Bai wa El-Zakzaky Izinin Tafiya kasar Turai don binciken Lafiyar Jiki

Shugaban ‘Kungiyar ci gaban Musulunci ta Najeriya (IMN) da aka fi sani da ‘Yan shi’a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya sami izinin tafiya zuwa kasar Turai don kula da lafiyar jikinsa da ta matarsa.

Naija News Hausa ta samu tabbacin hakan ne bisa umarnin da Kotun koli ta jihar Kaduna ta bayar a ranar Litinin, 5 ga watan Agusta a wata hukuncin da Mai shari’a Darius Khobo ya yanke.

2. Kotun Shugaban kasa: Abinda Kotu ta Bayyana ga Jam’iyyar HDP Game da Nasarar Buhari

Kotun daukaka kara ta Shugaban kasa a ranar Litinin da ta gabata, ta tanadi hukunci a cikin karar da Jam’iyyar Hope Democratic Party, HDP ta shigar a gabanta akan kalubalantar nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben shugaban kasa ta ranar 23 ga watan Fabrairu da ta wuce.

Ka tuna da cewa a baya, Jam’iyyar tare da wasu Jami’o’i sun bayyana rashin amincewa ga matakin Hukumar INEC na sanar da nasarar shugaba Muhammadu Buhari bisa sakamakon da suka gabatar.

3. Hukumar DSS Sun shirya da Sakin El-Zakzaky Da Matarsa

Shugaban ƙungiyar ci gaba da Harkar Musulunci ta Najeriya (IMN), Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matarsa ​​Zeenat za su shaka iskar ‘yanci ba da jinkirta ba, a yayin da hukumar tsaro ta DSS ke shirin tabbatar da sakinsa sa tare da matarsa.

Naija News ta fahimta da cewa wannan ci gaban ya biyo ne bayan da Mai shari’ar Kotun Koli ta jihar Kaduna, Darius Khobo, ya bada umarnin a saki El-Zakzaky da matarsa ​​Zeenat bayan shekaru a katangewar gwamnatin Tarayya a jagorancin shugaba Muhammadu Buhari.

4. Abin da ya zan Dole ga sabbin Ministocin Buhari da yi kafin rantsar da su – CCB

A yayin da ake shirin kadamar da hidimar rantsar da sabbi Ministocin da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar don fara aiki a ofishin su, Hukumar Code of Conduct Bureau (CCB) ta bukace su da su bayyana dukiyar su kamin lokacin rantsar da su ya gabato, ko kuma su shirya da fuskantar doka.

Naija News Hausa ta samu tabbacin hakan ne a wata gabatarwa da Shugaban CCB, Farfesa Muhammed Isah, ya bayar a lokacin da yake bayani game da ministocin.

5. #RevolutionIsNow: Dalilin da yasa muka watsar da Tear Gas ga masu Zanga-zangar – Yan sanda

‘Yan sanda sun ba da hujjar matakin da suka dauka na watsar da mugun hayaki mai sa hawaye da aka fi sani da ‘Tear Gas’ ga wasu masu zanga-zanga da ikirarin #RevolutionNow a birnin Legas

Kamar yadda Naija News da wasu rahotannai suka ruwaito a baya, jami’an tsaro sun ci karo da wasu daga cikin masu zanga-zangar a babban filin wasa da ke a jihar Legas.

6. Kasafin Kuɗaɗen da Gwamnatin Tarayya ta shirya don kashewa ga Ruga a shekarar 2019

Matakin dakatar da tsarin warware Ruga a kasar Najeriya da Shugaba Muhammadu Buhari yayi ya haifar da kwanciyar hankali da zamantakewar al’umma a kasar.

Bisa bincike da la’akari da wahayin da mai taimaka wa Shugaba Buhari, Ita Enang ya bayar, ya bayyana da cewa an ware naira biliyan 2.2b a cikin kasafin kudin 2019 don kafa Ruga.

7. Cin Mutunci Al’Umma – Gani Adams ya kalubalanci DSS a kan kama Sowore

Gani Adams, Aare Onakakanfo na Yarabawa, ya kafa bakin sa ga kiran neman a saki Omoyele Sowore, dan takarar shugaban kasa a zaben 2019 daga Jam’iyyar African Action Congress (AAC).

Ka tuna da cewa Hukumar DSS sun kama Sowore, wanda aka sani da zama shugaban gidan jaridar Sahara Reporters, akan wata Zanga-zanga da ya shirya da yi a dukan kasar.

8. IMN ta mayar da Martani ga matakin Kotu da bayar da damar ‘yanci ga El-Zakzaky da Matar sa

Ka tuna, kamar yada Naija News ta sanar a baya da cewa kotun koli ta jihar Kaduna a jiya Litinin, ta bayar da umarnin a saki Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matarsa ​​Zeenat don su tafi kasar Turai don binciken lafiyar jikinsu.

A cikin hanzari, Kungiyar IMN ta yaba wa umarnin kotun, da fadin cewa lalai wannan matakin ya bayyana nasara ga kudurinsu da kare kai yayin fuskantar zalunci.

Ka sami kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin NaijaNewsHausa