Uncategorized
Hukumar DSS sun Fyauce da El-Zakzaky da Matarsa da zarar sauka Jirgin sama
Rukunin Hukumar Tsaron Kasa ta Jiha da aka fi sani da (DSS), a yau Jumma’a sun fyauce jagoran Kungiyar Ci gaban Harkokin Musulunci ta Najeriya (IMN) da aka fi sani da ‘Yan Shi’a, Sheikh Ibraheem El-Zakzaky da Matarsa Zeenah da zarar isar su a kasar Najeriya.
Ka tuna mun sanar a Naija News Hausa a baya da cewa Ibrahim El-Zakzaky da Matarsa sun tafi kasar Indiya don binciken lafiyar jikin su.
Ko da shike da isar su a Indiya, bisa rahoton da aka bayar ga Naija News, da kuma yadda rahotannai suka bayar, El-Zakzaky ya ki yadda da Likitoci su bashi magani, a yayin da yake fadin cewa Likitocin sun banbanta da wadanda aka bashi daga Najeriya.
Bayan wannan jayayyar ne El-Zakzaky da Matar tasa, Zeenah, suka baro kasar Indiya da dawowa a Najeriya.
Naija News Hausa ta kuma gane da cewa a yayin isar El-Zakzaky da Matarsa a Filin Jirgi ‘International Airport ta birnin Abuja, missalin karfe 11:40 na safiyar yau, nan take Hukumar DSS suka dauke shi ba tare da jinkiri ba.