Labaran Najeriya
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a, 23 ga Watan Agusta, Shekara ta 2019
Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a, 23 ga Watan Agusta, 2019
1. Shugaba Buhari Yayi sabuwar Alkawari Ga ‘Yan Najeriya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis a birnin Zariya, jihar Kaduna, ya yi alkawarin cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da aiwatar da manufofi tare da aiwatar da ayyukan da mutane zasu ci amfanin sa da kuma wanda zai canza tsarin kasar Najeriya.
Shugaban da yake jawabi yayin zartar da aikin samar da Ruwar Bultsatse a Zariya, ya ce Gwamnatin Tarayya, duk da kasawa ga albarkatun kasa ta kashe Naira biliyan 11 da digo 8 a kan aikin gina madatsar ruwa ta Mita Miliyan 186.1 kan Dam ta Galma a matsayin gudummawa ga aikin.
2. ‘Yan Boko Haram Sun Shiga Garin Borno, sun kuwa Kone Ofishin INEC da Gidaje
‘Yan Ta’addan Boko Haram sun kai wata sabuwar hari a Gubio, wani gari a cikin jihar Borno, inda suka watsar da dubun mutanen garin a harin.
Bisa rahoton da Naija News ta karba a kan jaridar TheCable, majiyar mai tushe sun ce ‘yan kungiyar ta Boko Haram sun mamaye garin da misalin karfe 5 na yamma a ranar Laraba, 21 ga Agusta, da harbe-harbe, harma da kone gidajen mutane.
3. ‘Yan Sandan Jamus sun bayyana asalin wadanda suka kai hari ga Sanata Ekweremadu
Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Bavaria ta gano wadanda suka kai hari ga tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Dakta Ike Ekweremadu.
Ka tuna da cewa ‘Yan kungiyar IPOB da ke tuhumar Ekweremadu sun buge shi a cikin ziyarar da ya kai a Jamus, a kwanar baya.
4. Shugaba Buhari da hukumar INEC ta Samu Wani Babban Nasara A Kotun Shugaban Kasa
Kotun sauraren karar shugaban kasa a ranar Alhamis, ta yi watsi da karar da jam’iyyar adawa, watau Hope Democratic Party (HDP) da dan takaran su, Ambrose Owuru ya gabatar.
Naija News ta ruwaito a baya da cewa HDP da Owuru suna kalubalantar nasarar Shugaba Muhammadu Buhari da Jam’iyyar All Progressives Congress a zaben shugaban kasar da aka yi ranar 23 ga watan Fabrairu.
5. Sabuwar zance game da karar zargi tsakanin Busola Dakolo da Fasto Fatoyinbo
Wani sabon rahoto ya taso game da bincike akan zargin fyade da Busola Dakolo ke yi ga babban Fasto na Ikilisiyar Commonwealth of Zion Assembly (COZA).
Hadaddiyar Kungiyar Pentikostal ta tarayyar Najeriya, PFN ta bayyana cewa Fatoyinbo ya yi watsi da kwamitin da aka kafa don binciken zarge-zargen da ake yi game da shi.
6. Shugaba Buhari ya yi watsi da ritayar Oyo-Ita
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi watsi da ritayar gaggawa da Winifred Oyo-Ita, Shugaban Ofishin Ma’aikatan Tarayya ta yi.
Naija News ta fahimta da cewa Oyo-Ita ta dawo kan teburin jagorancin ta a ranar Alhamis, 22 ga Agusta, bayan da shugaba Buhari ya ki amincewa da ritayar.
7. An sace dan majalisar dokoki a jihar Sakkwato
An sace dan majalisar da ke wakiltar mazabar Denge / Shuni a majalisar dokokin jihar Sakkwato, Aminu Magaji Bodai.
Bisa rahoton da wani dan Uwa ga dan Majalisar ya bayar, ya bayyana da cewa ‘yan garkuwan sun sace shi ne misalin karfe 1:15 na safe tsakanin Dange da garin Bodai ranar Alhamis.
8. Wadume Ya tona Asirin Kyaftin Sojojin Najeriya
Sabuwar zance ta taso bayan da aka kame shahararren dan ta’adda da shugaban ‘yan fashi, Hamisu Bala (a.k.a Wadume) wanda aka sake kamawa a ranar Litinin.
Bayan sake kama shi, Wadume ya yi ikirarin cewa ya aika da kudade masu yawa ga kyaftin Sojojin wanda a baya ya tsara yadda aka sake shi daga hannun ‘yan sanda.
Ka sami kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com