Uncategorized
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina sun Ceci Mata 10 daga hannun ‘Yan Fashi
Naija News Hausa ta karbi rahoton yadda Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ceci Mata 10 cikin 15 daga hannun ‘yan fashi, wanda suka sace a safiyar ranar Talata da ta gabata a kauyen Wurma da ke karamar Hukumar Kurfi ta jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASP Anas Gezawa, a ranar Laraba a Katsina ya bayyana da cewa “‘yan hari da bindiga sun mamaye kauyen Wurma da ke karamar hukumar Kurfi a inda suka sace wasu mata 15, a cikin su ne kuwa tare da diyar Hakimin kauyan da kuma surukin sa daya.
Gezawa, a cikin bayanin sa ya bayyana da cewa barayin sun kwato dabobi, musanman shanaye mara iyaka daga yankin.
“Rundunar ‘yan sandan Jihar sun ceci 10 daga cikin mata 15 da aka sace. Tun lokacin kuwa aka mikar da su ga danginsu. Harwayau kuwa jami’an tsaro na kan kokarin ribato sauran matan da kuma kame masu aiwatar da mumunar harin” inji Gezawa.