Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a 30 ga Watan Agusta, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a 30 ga Watan Agusta, 2019

1. Kotu ta Fidda Tsohon Ma’aikaci ga Jonathan daga Dukan Karaki na Cin hanci da rashawa

Tsohon babban Mashawarci ga tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan, akan harkokin kasa ta gida,  Waripamo-Owei Dudafa, da wani da kuma ma’aikacin Banki Joseph Iwuejo, wadanda ake zargi da satar N1.6bn sun kubuta daga dukkan tuhumar cin hanci da rashawa da ake yi da su.

An bayyana hakan ne a wata hukuncin da mai shafi 190, wanda Mai shari’a Mohammed Idris ya fada ga hukumar EFCC da cewa ta gaza gabatar da tabbatar da tuhumar da ya taka-kara da karewa guda 22 bisa Owei-Dudafa da Joseph Iwejuo.

2. Maiyiwuwa El-Zakzaky da Matar su bar kasar Najeirya zuwa kasar waje don kara binciken Lafiya jiki

Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, shugaban kungiyar Harkar Musulunci a Najeriya, da matar sa, Zeenat, na a shirye don sake wata tafiyar zuwa kasar Turai bada jimawa ba.

A bayanin da wani babban jigo a Kungiyar ‘Yan Shi’a ya bayar, ya bayyana cewa ba da jimawa ba za a fitar da shugabansu zuwa kasar Turai don binciken lafiyar jikin sa,  amma har yanzu ba a bayyana ranar ba.

3. Diezani na shirye don fahimtar mataki na gaba a Ranar 2 ga Satumba

An gabatar da ranar 2 ga watan Satumba 2019 ta gaba don yanke hukunci na karshe akan mallakar kayan ado mai tsadar dala $40m da aka gane da tsohuwar ministar albarkatun man fetur na Najeriya, Diezani Allison-Madueke.

Naija News ta fahimci hakan ne a wata sanarwa da Mai shari’a Nicholas Oweibo ya ba da game da  dagewa ga sauraron karar da aka yi a ranar Alhamis da ta wuce.

4. Mahara da bindiga Sun Kashe Firist na Katolika a Taraba, sun kona shi da motarsa

Wasu da ake zaton su da zama ‘yan hari da bindiga ta kungiyar Tiv sun kashe wani Firist na cocin Katolika, suka kuwa haska wa motarsa wuta a garin Kufai Amadu, karamar hukumar Takum ta jihar Taraba.

An bayyana da cewa firist din na kan hanyarsa ta zuwa taron sulhu tare da sauran Wakilan coci ne kan yadda za a warware rikicin da ke tsakanin ‘yan Tiv da Jukun yayin da maharan suka kashe shi.

5. Buhari ya mallaki ra’ayin ‘yan Shari’a da Majalisar Tarayya a Karkashinsa – Buba Galadima

Wani jigon jam’iyyar Peoples Democratic Party, Buba Galadima, ya zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da mallakar bangaren shari’a da majalisar dokoki ta kasa “gaba daya a karkashin sa.

Galadima yayin da yake Magana a kan hidimar Siyasa a gidan Talabijin na Channels a ranar Alhamis, ya zargi Shugaban kasar da tsoratar da bangaren hukumar shari’a, ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani game da ikirarin cewa wasu “abokan wannan gwamnatin” suna kokarin yin kadamar da makirci a kasar shugaban kasa a kotu.

6. EFCC ta kame mutum 4 akan ayyuka masu tsadar  $16b na wutan Lantarki da Obasanjo ya jagoranta

Hukumar Yaki Cin Hanci da Rashwa da kuma kare Tattalin Arzikin kasa (EFCC) ta tsare mutane hudu dangane da binciken da ta yi kan ayyukan dala biliyan 16 a karkashin gwamnatin Shugaba Olusegun Obasanjo, a shekarun baya da suka gabata.

Naija News ta fahimci cewa manyan jami’ai biyu na Kamfanin Neja Delta Power Holding Company (NDPHC), kamfanin da ta jagorancin hidimar aikin suna daga cikin mutane hudun da hukumar EFCC ta tsare.

7. Muna da sabon dabarun da zasu tilastawa ‘yan Boko Haram su mikar da kansu – Sojoji

Rundunar Sojojin Najeriya sun sanar da cewa suna da wani sabon tsari da zai kai ga tabbacin tilasta ‘yan ta’addar Boko Haram da ke fargaba don janyewa daga ayukansu da mikar da kansu da tsaro.

Sojojin sun bayyana hakan ne a wata bayani da Kwamandan Rundunar Sojojin Najeriya na Birgediya ta 7, Janar Abdul Khalifa Ibrahim ya bayar.

8. Ganduje ya bayyana Gwamnonin da ke hada kai don tsanantawa Oshiomhole

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana shirin wasu gwamnonin jam’iyyar All Progressive Congress (APC), akan kokarin cire shugaban jam’iyyar na kasa, Adams Oshiomhole daga kan kujerar jagorancin sa.

Wannan bayanin ne Ganduje ya bayyana a wani zaman tattaunawa da yayi da manema labarai a Abuja ranar Alhamis, lokacin da ya bayyana cewa ba zai taba shiga cikin irin wannan makircin ba.

Ka sami kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin NaijaNewsHausa