Uncategorized
Ambaliyar Ruwa ya Tsinke Gidaje Kimanin 2667 a Jihar Neja
Naija News ta samun tabbacin cewa akalla gidaje 2,667, gonaki, hanyoyi, gadoji ne ambaliyar ruwa ta tsinke da su a kananan hukumomi 17 da na jihar Neja.
Tabbacin hakan ya bayyana ne a yayin wata gabatarwa na tattaunawa da Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa na jihar Neja (NSEMA), Alhaji Ahmed Inga yayi a Minna, babban birnin jihar Neja a ranar Alhamis.
Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Gwamnatin Jihar Neja tayi Ikirarin cewa An yi Kusa da Karshe Gyaran Babban Hanyar Minna zuwa Suleja.
Jagoran hukumar NSEMA, Mista Inga ya bayyana da cewa da yawar gidaje, hanyoyi da gadoji ne ambaliyar ruwan ya lallace a kananan hukumomin Jihar.
“Haka kazalika ambaliyar ya shafi wuraren kiwon dabbobi, hanyar bin ruwar (kwalbati), makarantun firamare, asibitoci, tafkunan kifaye, da wuraren kiwon lafiya” inji Shi.
Naija News Hausa ta gane da cewa yawar ruwan sama a Jihar ne ya kawo sanadiyar ambaliyar.
Hukumar NEMA DG ta ce lamarin ya faru ne tsakanin watan Agusta da Satumba, kuma ta kara da cewa hukumar na ci gaba da karbar karin rahoto game da aukuwar ambaliya a jihar a halin da ake ciki.
Wadannan ne bangaren da ambaliyar ya shafa, bisa bayanin sa; Rafi, Gurara, Paikoro, Suleja, Agaie, Katcha, Kontagora, Gbako, da Shiroro. Sauran wuraren da abin ya shafa kuma sun hada da Bosso, Chanchaga, Mashegu, Edati, Lavun, Lapai da Mokwa.
Ko da shike dai Daraktan ya bayyana da cewa hukumar su ta riga ta samar da rahoton yanayin ga Ofishin Gwamnan Jihar, Abubakar Sani Bello (LoLo), don daukar mataki ta musanman kamin abin ya kara yawaita da mumunar barna a Jihar.