Uncategorized
Gwamnatin Tarayya ta sanar da Hutu Don Yin Bikin Ranar karban ‘Yanci ga kasar Najeriya
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ayyana ranar Talata, 1 ga Oktoba, a matsayin ranar hutu ga jama’a duka don hidimar bikin cika shekaru 59 ga samun ‘yancin kai.
An sanar da hakan ne ta bakin Sakataren din din din din na Ma’aikatar Aikin Gida, Misis Georgina Ehuriah, cikin wata sanarwa a ranar Laraba a gurbin Ministan Hukumar.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Gwamnan jihar Kaduna, Nasir-El-Rufai ya jefa dan nasa, Abubakar Al-Siddique El-Rufai a makarantar firamare ta gwamnati a jihar.
Bisa rahoton da Naija News ta tattara, Gwamnan ya sanya Al-Siddique ne a Aji na Farko a Firamare ga makarantar Kaduna Capital School ranar Litinin.
Ko da shike jita-jita ya biyo daga baya daga wasu manyan Ma’aikata da kuma ‘yan Siyasa da cewa El-Rufai yayi hakan ne kawai gabadin zaben shugaban kasa ta shekarar 2023.
Ka kuwa tuna a baya da cewa an fito da wata kalandar da ke dauke da hoton Gwamna Nasir El-Rufai hade da jagoran hidimar neman zabe ga tarayyar jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole, da nunin su a matsayin ‘yan takara ga neman kujerar shugaban kasa a shekara ta 2023.
Kalli Hotona kasa;