Labaran Najeriya
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a, 27 ga Watan Satumba, Shekara ta 2019
Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a, 27 ga Watan Satumba, 2019
1. Gwamnatin Tarayya zata Sake Tsarin Karancin Albashin Ma’aikata
Gwamnatin Tarayya Najeriya na batun sake tsarafa kungiyarta a kwamitin hadin gwiwar bangarorin jama’a (JPSNC) kan aiwatar da sabon mafi karancin albashi na N30,000.
Naija News ta fahimci cewa kungiyar wacce ke karkashin jagorancin tsohon shugaban hukumar aikin farar hula (HoCSF) Misis Winifred Oyo-Ita za a sake zama a yau Juma’a, 27 ga Satumba don canza tsari.
2. Obasanjo Ya Ziyarci Shugaban Kasar South Afirka don Tattaunawa kan hare-hare ‘Yan Najeriya
Tsohon Shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya ziyarci Shugaban kasar South Afirka, Cyril Ramaphosa, ‘yan makwanni bayan harin Xenophobic da aka yi kan’ yan Najeriya a kasar South Afirka.
Naija News ta fahimta da cewa ziyarar ta zo ne bayan wasikar da Obasanjo ya aika wa Cif Mangosuthu Buthelezi, dan siyasar kasar South Afirka da kuma shugaban kabilan Zulu game da matsalar hare-haren.
3. Shugaba Buhari Ya Mayar da Martani game da Rufe Bodar Najeriya
Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta hannun kwamandan Rundunar Kwastam ta Najeriya (NCS) mai ritaya, Col. Hameed Ali, ta ce an dauki matakin rufe bodar Najeriya ne don karfafa tsaron kasar da kare bukatun tattalin arzikinta.
Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta bayar da rahoton cewa Ali ya sanar da hakan ne yayin ganawarsa da masu ruwa da tsaki kan bodar, wadanda suka hada da masu jigilar kayayyaki da hukumomin tsaro ranar Alhamis a Seme.
4. #RevolutionNow: Me Yasa Har Yanzu Ba ‘a Saki Sowore ba – DSS
Ma’aikatar Tsaron Jiha-da-Jiha ta kasa (DSS) ta bayyana dalilin da ya sa har yanzu ba a saki jagoran kungiyar zanga-zanga ta #RevolutionNow, Omoyele Sowore ba.
Naija News ta tuna cewa Babban Kotun Tarayya, Abuja, ta yi barazanar daure Darekta-Janar na DSS, Yusuf Bichi, game da tsare Sowore da tsawon lokatai.
5. Boko Haram: Buhari Ya Yi Allah Wadai da Kashe Ma’aikatan agaji da ISWAP suka yi
Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da kisan daya daga cikin ma’aikatan agaji shida da aka yi garkuwa dasu ta hannun kungiyar Islamic State a kasar South Afirka da aka fi sani da (ISWAP).
Naija News fahimta da cewa ‘yan ta’addar Boko Haram sun kashe daya daga cikin ma’aikatan agaji da aka sace a jihar Borno.
6. Jam’iyyar APC ta mayar da Martani game da rikice rikicen da ke Afkuwa a Shugabancin kasar
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC), jam’iyyar da ke mulkin Najeriya, ta yi watsi da jita-jitan da zancen wata rashin jituwa tsakanin Shugaba Muhammadu Buhari da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo.
Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta bayar da rahoton cewa, jam’iyyar da ke kan karagar mulki ta dage da cewa babu wani rikici da ke afkuwa a Fadar Shugaban kasa kamar yadda aka ruwaito a wani sashe na kafafen yada labarai na Najeriya.
7. Karancin Albashi: Kungiyar Ma’aikata sun gabatar da Sabuwar zance ga Gwamnatin kasar
Wani bangare na kungiyar kwadago a Najeriya sun koka kan ci gaban jinkirtan aiwatar da mafi karancin albashi na N30,000 ga ma’aikatan Najeriya.
Kungiyar kwadagon ta bukaci a biya albashin ma’aikatan kamar yadda ta ke a da kamin fara biyan mafi ƙarancin albashi wanda ake jinkirta da shi.
8. Rikici a Shugabancin Kasa: Ina Kuwa Tausaya wa Tinubu – Mike Ozekhome
Babban Lauyan fafutukar Kasa, Mista Mike Ozekhome, ya bayyana cewa yana tausayawa Shugaban jam’iyyar APC, Bola Tinubu.
Mike, Mai kare hakkin dan adam ya bayyana cewa rukunonin da ke a cikin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na shirin tsige Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo, bayan sun yaudare shi da amfani da shi wajen rarraba Tradermoni ga ‘yan kasuwa kamin babban zaben da ya gabata.
Karanta Kari da Cikakken Labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa