Uncategorized
Kotu ta Isar da hukuncin karshe akan zaben Tambuwal
0:00 / 0:00
Kotun daukaka karar zaben Sakkwato a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya ta tabbatar da zaben gwamna Aminu Tambuwal na Jam’iyyar PDP, babbar jam’iyyar adawa a Najeriya.
Naija News ta sanar da fahimtar cewa Kotun daukaka kara a Sakkwato ta gabatar da hukuncin karshen ne game da zaben gwamna na Sakkwato a ranar Laraba, 2 ga Oktoba.
Wannan rahoton ya biyo ne bayan da Kotun ta yi watsi da karar da Ahmed Aliyu da jam’iyyar All Progressives Congress (APC), jam’iyyar da ke mulkin Najeriya suka kalubalanci ayyana Gwamna Tambuwal a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a ranar 9 ga Maris, kamar yadda Hukumar gudanar da Zaben kasa (INEC) ta sanar.
KARANTA WANNAN KUMA; Sanata Kwankwaso ya tallafawa daliban Kano 242 ga zuwa Karatu a Turai.
© 2025 Naija News, a division of Polance Media Inc.