Connect with us

Uncategorized

Sojojin Ruwa ta Najeriyar Sun ta Fitar Fom na Daukar Ma’aikatar [DSS] Na shekarar 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Rundunar Sojojin Ruwa ta Najeriya ta fara aiwatar da daukar ma’aikata ga shiga rundunar amma a karkashin ‘Direct Short Service Commision (DSS)’.

Naija News ta sami tabbacin hakan ne bisa wata sanarawa da aka bayar a ranar Laraba ta bakin Daraktan watsa labarai na rundunar sojojin ruwar, Commodore Suleman Dahun a birnin Abuja.

A cikin bayanin Dahun, ya ce, “masu neman shiga aikin dole ne su kasance ‘yan Najeriya ta hanyar haihuwa, ya kamata kuma su mallaki mafi karancin maki na ‘Second Class Upper’ ga karatun Digiri na Farko (Bsc) ko kuma ya kare Karatun sa a Makarantar Jami’ar Fasaha babba (HND).

“Maza masu neman shiga ya zama dole su kasance da tsayi daga mita 1.68 zuwa sama, yayin da masu neman mata ya zan dole suma su kasance da tsayi na karancin mita 1.65.

“Masu neman aiki dole ne su mallaki takardar shedar bautar kasa ta NYSC  ko ta Yancin Siyarwa daga bautar (Excemption Certificate), kuma ya kamata su kasance tsakanin shekara 22 zuwa 28 ne ga haifuwa daga ranar 20 ga watan Fabrairu, 2020.”

Dahun ya baiyana da cewa za a rufe fagen cika fom din ne a ranar 14 ga Nuwamba, 2019 ga masu son shiga aikin.

Ka shiga layin NaijaNews.Com don gane layin cika fom din da karin baiyanai kuma.