Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba 2 ga Watan Oktoba, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba 2 ga Watan Oktoba, 2019

1. Yan Najeriya zasuyi ci Amfanin Wutar Lantarki mara Yankewa – inji Buhari

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya yi wa ‘yan Najeriya alkawari da tabbacin cewa kasar za ta more wadataccen wutar lantarki mai tsafta ba tare da tsawa ba a nan jin kadan.

Naija News ta fahimci cewa shugaban ya yi alƙawarin ne yayin jawabinsa a ranar ‘Yancin Kai ta shekara 59. A cewarsa, gwamnatin Najeriya a jagorancin sa na shirye don samar da isashen wutar lantarki ga jama’a.

2. Shugaba Buhari Ya Bar Abuja Don ziyarar kasar South Afirka

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shirya da barin birnin Abuja ranar Laraba yayin da zai ziyarci kasar South Afrika da tsawon kwanaki uku.

Naija News ta fahimta da cewa ziyarar ya biyo ne bayan wasikar gayyata da shugaban South Africa, Cyril Ramaphosa ya aika wa Buhari don tattaunawa kan zamantakewar ‘yan Najeriya da ke zama a kasar.

3. Bafarawa ya zargi Tinubu da haifar da matsala a APC

Tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Attahiru Bafarawa, ya bayyana cewa rikicin shugabancin All Progressives Congress ya afku ne sanadiyar muradin Shugaban Jam’iyyar na kasa, Bola Tinubu, da ya mallaki jam’iyyar gaba daya.

Bafarawa, yayin da yake zantawar da manema labaran Guardian ya kara da cewa “rashin gaskiya da amincin Tinubu da sauran shugabannin jam’iyyar APC” ne sanadiyar rikicin da ke afkuwa a cikin jam’iyyar.

4. Nigeria @59: Aisha Buhari ta bayyana shirinta ga Najeriya

Uwargidan shugaban kasan Najeriya, Malama Aisha Buhari, ta yi baiyana shiri da burinta ga makomar Najeriya a yayin da kasar ta cika shekaru 59 da yancin kai.

Duk da cewa matar shugaban ba ta dawo kasar ba tun lokacin da aka kammala aikin Hajji a Saudiyya, Aisha ta ce ta dage da burin bautar kasar ta hanyar taimaka wa gajiyayyu.

5. Shugaba Buhari Ya shirya da Hukunta Ma’aikatan kwastom, FIRS, da Sauransu saboda gaza ga cikar Manufa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na ganin an samu ci gaba ta fanin raya Tattalin Arziki da kuma habbaka a Najeriya.

Don haka, Shugaban ya ce hukumomin da ke samar da kudade ga gwamnatin za su kasance cikin sahihan bincike a nan gaba.

6. INEC ta fitar da sunayen ‘yan takarar ga zaben Gwamnonin Bayelsa

Hukumar gudanar da Zaben kasa, INEC ta fitar da jerin sunayen ‘yan takarar karshe da aka tantance wadanda za su fafata a zaben gwamna na jihar Bayelsa.

An bayar da Jerin sunayen ne a kunshe cikin wata sanarwa a ranar Talata wanda Naija News ta samu daga layin Twitter na INEC.

7. Najeriya A 59: Kalubalen Najeriya Matsaloli ne mai kai mu ga Nasara – in ji Lawan

Shugaban majalisar dattijai, Ahmed Lawan, ya ce kalubalen da Najeriya ke fuskanta matsaloli ne da zasu kai kasar ga cin nasara ta musanman.

Naija News ta fahimci cewa Shugaban Majalisar Dattawar ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya yi don bikin ranar samun ‘yancin kai na Najeriya ta shekara 59.

8. Najeriya A 59: Dalilin da yasa Na kafa Majalisar Ba da Shawara kan Tattalin Arziki – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya kafa sabon kwamitin ba da shawara kan tattalin arziki (EAC) ne domin su yi ta yi masa nasiha game da manufofin kasafin kudin kasar.

Wannan bayanin shugaba Buhari ya fito ne a ranar Talata yayin watsa jawabinsa lokacin bikin ‘yancin kai ga ‘yan Najeriya.

9. Shugaba Buhari Ya Ba da umarnin Sakin N600bn Domin Ayyuka ga Kasar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci Ministar Kudi, Misis Zainab Ahmed da ta saki naira biliyan N600 domin kashe kudaden ga manyan ayuka a kasar a cikin watanni uku masu gabatowa.

Naija News ta fahimci cewa an ba da wannan umarni ne a yayin sakon tunawa da shekaru 59 na ‘yancin kai ga ‘yan Najeriya a ranar Talata a birnin tarayya, Abuja.

Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya ta yau a shafin Naija News Hausa