Connect with us

Uncategorized

Gwamnan Jihar Jigawa, Badaru ya Sanya Mataimaka ga Matanshi Uku

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar ya nada mataimaki na musamman ga kowane daya daga cikin matansa Uku.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa a cikin mataimaka na musamman 51 da gwamna ya nada a Jihar, akwai kuma mataimaki na musamman kan hasken wutan tituna da kuma kula da alumma.

Bisa kwafin jerin sunayan wadanda Gwamnan ya nada da manema labaran Daily Trust suka bayar, an nuna cewa Sa’adatu Bashir Muhammed ce mataimakiya ta musamman ga matar gwamnan na farko, yayin da Mariya Muhammed Muktar da Aisha Garba mataimakan na musamman ne ga na biyu da na ukun matan Badaru.

Haka kazalika jerin sunayan ya bayyana Hassan Usman Bulama da Surajo Musa Gwiwa a matsayin mataimakan musanman ga gwamna kan hasken wutan tituna da kuma kula da yawan jama’a.

Naija News Hausa ta kula da cewa a bayyane ne ayukan duk mataimakan da gwamnan ya gabatar, amma ba tabbacin aikin da mataimaka na musamman guda uku ga matan gwamnan za su yi.

KARANTA WANNAN KUMA; Dalilin da Yasa Shugabancin Najeriya Ba Zai Yiwu Ba ga Iyamirai – Wabara