Dalilin da Yasa Ba Zai Yiwu Ba ga Iyamirai da Shugabanci Kasar Najeriya – Wabara

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Adolphus Wabara ya yi ikirarin cewa babu damar Shugabancin kasar Najeriya ga Iyamirai a shekarar 2023.

Ya bayyana da cewa an riga an sanya tsare-tsare, raunanar karfi da tsananci ga Nndigbos a hidimar siyasa, musanman a fifikon kabilanci da burin neman shugabancin kasar a cikin shekaru hudu masu zuwa.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Sanatan da ya wakilci Jihar Kaduna a Majalisar Dattajai na takwas, Sanata Shehu Sani ya gargadi Arewa da su manta da zancen neman shugabancin kasar Najeriya a zaben shugaban kasa ta 2023 da ke a gaba.

“Ku manta da batun neman wanda zai maye gurbin shugaba Muhammadu Buhari a shugabancin Najeriya a zaben shugaban kasa ta 2023” inji Shehu Sani a wata ganawa da yayi kwanakin baya da manema labarai a garin Minna, babban birnin Jihar Neja, inda ya fada da cewa lallai Arewa ta lashe kashinta a shugabanci shugaba Muhammadu Buhari.