Connect with us

Labaran Najeriya

Abinda Shugaba Muhammadu Buhari ya Fada A Taron Rasha

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi jawabi ta musanman a taron farko na taron Rasha da Afirka da aka yi a kwanan baya.

Naija News Hausa ta sanar a baya da cewa shugan zai tafi kasar Rasha don halartar wata taro.

A ranar Alhamis din da ta gabata, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, Najeriya na fatan ta rungumi sabon salo na hadin gwiwar Afirka da kasar Rasha da kuma sake farfado da dangantakar Najeriya da Rasha.

Ka tuna da cewa Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, a ‘yan kwanaki da suka gabata ya tafi kasar China don binciken sabbin Jiragen Kasa da Injiniyoyin Fasahar kasar China suka kirkira wa Najeriya don amfani matafiya.

Amaechi ya gana da wasu jami’an ma’aikatar CCRC, inda ya gwaji daya daga cikin manyan jirage biyu da aka kirkira a kamfanin CCRC ta harabar gundumar Qisuyan, Changzhou, China.