Uncategorized
Kungiyar Kamfanin Dangote ta fara kafa kamfanin sarrafa Shinkafa a Jihar Kebbi
A ranar Lahadin da ta gabata, Gwamna Atiku Bagudu, gwamnan jihar Kebbi ya yaba wa rukunin kamfanonin Dangote saboda kafa kamfanin sarrafa shinkafa a jihar, yana mai cewa hakan zai samar da aikin yi da bunkasa tattalin arzikin kasar.
Bagudu a yayin da ya ziyarci matattarar masana’antar da aka kafa a Saminaka, a karamar hukumar Shanga ta jihar, ya ce wannan zubar da jari da kamfanin ta yi a jihar zai darajarda shinkafa tare da kara daraja ga manoman yankin.
An sanar da ziyarar Gwamnan ne ta bakin Sakataren yada labaran sa, Abubakar Dakingari a wata sanarwa a ranar Lahadi a Birnin Kebbi.
Naija News ta fahimta da cewa masarrafar mai dauke da silas 32 da aka kafa a jihar, ya sami karban ziyarar Gwamna Bagudu wanda ya samu rakiyar shugabannin majalisa da manyan jami’an gwamnatin jihar.
“Dole ne in yaba wa rukunin Kamfanoni na kamfanin Dangote, musamman Alhaji Aliko Dangote, saboda fara irin wannan ayyukan a Jihar Kebbi.” inji Gwamnan.
“Wannan zai taimaka sosai wajen samar da aikin yi ga matasanmu tare da bunkasa tattalin arzikin jihar da kuma Najeriya baki a daya.”
Bagudu ya yi amfani da damar wajen gayyatar ƙarin masu zuba jari zuwa Kebbi don kafa masana’antu. Hakanan, gwamnan ya tsaya a wani gidan sarrafa shinkafa da ke garin Yauri, inda ya yi hulɗa da wasu mata da ke sarrafa shinkafar gida.
Matan sun fada wa gwamnan cewa farashin shinkafa ya fadi, wanda a cewarsu, hakan wata alama ce da ke nuna cewa Gwamnatin Tarayyar Najeriya na shirin kwarai kan shinkafa.