Uncategorized
An Kame Dan Sandan Karya a Jihar Kogi a Yayin Hidimar Zabe Gwamnoni
Rundunar ‘yan sandan Najeriya da ke a yankin Igala Unity Square a Anyigba, karamar hukumar Dekina da ke jihar Kogi ta kama wani jami’in‘ yan sanda na karya.
Naija News ta samu labarin cewa dan sandan karyar da aka kame na sanye ne da T-shirt baki da wando na baki da wata jaket, ita ma baka mai dauke da rubutun SARS a jikinta.
Wata tawaga ta jami’an kwantar da tarzoma na musamman da suka yi sintiri a yankin sun tare mutumin ne da tambayoyi, anan aka gane da cewa shi ba dan sanda ba ne kamar yadda ya yi ikirarin kasancewarsa kuma nan da nan aka kama shi aka dauke shi cikin bas.
Ka tuna da cewa Tsohon Shugaban kasar Najeriya, Dr. Goodluck Jonathan ya bayyana damuwarsa gabanin zaben gwamnoni a jihohin Kogi da Bayelsa da aka shirya ranar Asabar.
Tsohon Shugaban wanda ya koka da yawan rikice-rikice da rahotannin tashin hankali da ya riga ya gudana tun kafin zaben, ya yi kira da a kame kuma a kwantar da hankulan dukkan masu ruwa da tsaki.