Uncategorized
Gobarar Motar Tanki Ya Tafi da Rayuka 5 a Jihar Kogi
Rahoton da ke isa ga Naija News daga manema labarai ya bayyana da cewa a kalla mutane biyar suka mutu, wasu kuma da raunuka yayin da motar tankin da ke dauke da man fetur rutsa da wasu motoci cikin Kogi.
A haka wannan al’amarin ya sanya mutanen Felele da ke a karamar Hukumar Lokoja cikin zaman makoki da jinya bayan a kalla mutane biyar ne aka ruwaito sun mutu sakamakon hatsarin da ya afku da motar tankin.
Naija News Hausa ta gane da cewa Hadarin ya afku ne a kan titin Lokoja-Okene-Abuja a safiyar ranar Litinin, inda m otoci da yawa suka hade har da Keke Napeps suka kone da wuta sakamakon gobarar da ta tashi.
Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewa direban motar tankin ya kasa ga shan karfin motar, a garin gwagwarmaya da motar ne ta ratsa a cikin tashar gidan mai na NNPC.
Wannan mumunar hadarin ya kai ga sanadiyar konewar wasu motoci da ke a kewayen, hade ma da Keke Napep da wasu babura a kusa da wajen.
An hango jami’an hukumar kiyaye haddura ta Tarayya suna kokarin kwashe gawakin wadanda suka mutu yayin da aka tafi da wadanda kuma suka jikata a asibitin da ke a Lokoja.
Lamarin ya haifar da rufe yawancin tashoshin gidan man fetur da ke a shiyar.
Kalli Bidiyon a Kasa;