Connect with us

Labaran Najeriya

Bello: Ga Bayanin Shugaba Muhammadu Buhari bayan Nasarar APC a Jihar Kogi

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Shugaba Muhammadu Buhari ya Mayar da Martani kan Nasarar Bello A zaben Gwamnonin Kogi

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a ranar Litinin, ya taya gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi murnar da sake zabensa a zaben gwamnoni na ranar 16 ga Nuwamba a jihar da aka yi.

A cikin wata sanarwa da mai ba da shawara na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Femi Adeshina ya bayar, Shugaban ya bayyana zaben fidda gwani da ficewar da dan takarar All Progressives Congress (APC) Yahaya Bello yayi a matsayin “tsere mai kyau da nasara.”

A yayin hakan, Buhari ya nuna tausayawarsa ga iyalan wadanda suka rasa kaunatattunsu a sakamakon tashin hankali da ya afku a lokacin zaben, Shugaban ya kuma yabawa magoya bayan jam’iyyar ta APC saboda tsayin daka da jajircewa duk da irin tashe tashen hankulan da ke faruwa.

Ya jinjinawa jami’an Hukumar Gudanar da Zaben Kasa (INEC) da hukumomin tsaro bisa sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.

Shugaba Buhari gargadi Gwamna Bello da ya yi amfani da wa’adinsa na biyu a kan mulki don gina tushen da aka kafa da kuma don inganta rayuwar jama’ar jihar Kogi.

Ka tuna Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Dan takarar gwamna na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben gwamna ta ranar 16 ga Nuwamba a jihar Kogi, Engr. Musa Wada, ya yi watsi da sakamakon zaben da hukumar INEC ke sanarwa.

Wada da abokin karawarsa sun bayyana da cewa akwai makirci a cikin sakamakon zaben da INEC ta riga ta sanar don taimakawa wa Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da dan takarar ta, Yahaya Bello.