Connect with us

Uncategorized

Sabuwa: ‘Yan Garkuwa sun Sace A Kalla Mutane Shidda a Jihar Kaduna

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Rahoton da ya isa Naija News Hausa a wannan lokaci ya bayyana da cewa wasu ‘yan garkuwa sun sace mutane biyar hadi da wata macce da ke kan renon danta a Jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne a Unguwar Dan Mani, karamar hukumar Igabi ta jihar, labarin faruwar ya baiyyana ne ga jama’a a ranar Laraba da daddare, da cewa ‘yan hari da bindigar sun kutsa cikin yankin da harbe-harben bindiga ko ta ina.

Shugaban wata karamar hukuma, wanda ba ya son a gabatar da sunansa, ya tabbatar wa manema labarai na jaridar Daily Post yadda abin ya faru. Yana mai cewa dukan jama’ar garin na cikin rawar jiki saboda mumunar harin.

Ya ce maharan sun fada wajen ne da harbi ko ta ina da tsakar daren a yayin da suka bi gida-gida suna daukar duk wanda suka yi ra’ayi sacewa.

“A yanzu haka muna cikin rudani saboda wadanda aka sace din maza hudu ne da mata biyu. A cikin matan akwai wata mata da ke kan renon diyarta, kuma sananna ce a cikin wannan al’umma da suna Matar Ghali. Sun tafi da ita yayin da mijin Ghali ya tsere. Gambo da Bukar suna cikin wadanda aka sace. Duk wadannan mutane talakawa ne. A haka mun gano da cewa mutane shida ne aka sace,” inji shi.

Ya kara da cewa ‘yan garkuwan sun kira matan daya daga cikin mazan da aka sace da cewa ta biya kudi Naira Biliyan Goma (N10m) kamin su saki mijin.