Connect with us

Uncategorized

Dino/Smart: INEC ta Sanar da Ranar Karshe Zaben Jihar Kogi

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar Gudanar da Zaben Kasa (INEC) ta sanya ranar Asabar, 30 ga Nuwamba, don gudanar da zaben lashe kujerar Sanata a Yammacin Kogi.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta bayar da rahoton cewa hukumar zaben ya tsaida ranar da za a gudanar da zaben ne a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar alhamis da yamma ta hannun Festus Okoye, kwamishina na kasa kuma Shugaban Kwamitin Yada Labarai da Kwamitin Ilimin masu jefa kuri’a.

Sanarwar ta kuma ce bayar da cewa hukumar za ta gudanar da zaben cike gurbi don mazabar tarayya ta Ajaokuta.

INEC ta yi kira ga jam’iyyun siyasa da masu ruwa da tsaki da su hada hannu da Hukumar don gudanar da zabuka masu inganci a cikin yankunan da abin ya shafa.

Ku tuna kamar yadda Naija News Hausa ta sanar a baya da cewa Sanatan mai wakiltar mazabar Kogi West Senatorial, Dino Melaye ya ziyarci hedikwatar Hukumar Zabe ta kasa (INEC) don neman a soke zaben ranar 16 ga Nuwamba a gundumar.

Dino a isarsa Ofishin ya samu marabta daga hannun Sakataren INEC, Rose Orianran-Anthony da kwamishina na kasa / Shugaban Kwamitin yada labarai da kwamitocin Ilimin masu jefa kuri’a, Festus Okoye.