Connect with us

Uncategorized

Kogi: Hukumar INEC Ta Baiwa Gwamna Bello Takardar Shaidar Nasara da Jagoranci

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar da ke gudanar da hidimar zaben kasa (INEC) ta bayarwa dan takarar gwamna a jam’iyyar All Progressives Congress a jihar Kogi, Yahaya Bello da abokin karawarsa Edward Onoja Takaddun shaida na Komawa kan mulki a ranar Alhamis.

Hukumar zaben a yau Alhamis ta bayar da takardar shaidar komawa kan kujerar gwamnan jihar Kogi ga Yahaya Bello, a nan dakkin bikin Farfesa Mahmoud Yakubu, a hedikwatar hukumar zaben da ke a Lokoja, babban birnin jihar.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Dan takarar jam’iyyar APC, Yahaya Bello ya samu yawar kuri’u 406,222 don kayar da dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party, Musa Wada, wanda ya samu kuri’u 189,704.

Kwamishinan hukumar na kasa wanda ke lura da yankin Arewa ta Tsakiya, Mohammed Kudu Haruna, wanda ya gabatar da takardun shaidar ga zababben gwamnan ya ce, “Yau ne sabon wa’adi ya fara bayan kamala zaben da kuma kira zuwa ga jagoranci ga zababban gwamna da mataimakin nasa.”