Connect with us

Uncategorized

Wani Fasto Ya Fantsama Ya Mutu jim kaɗan da Komawa Jam’iyyar APC a Edo.

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Naija News Hausa a safiyar ranar Jumma’a, yau ta karbi rahoton wani malamin cocin da aka bayyana a matsayin Fasto Aimola John, yadda ya fantsama ya kuma mutu jim kadan bayan ya hada kai da Fasto Osagie Ize-Iyamu da komawa Jam’iyyar All Progressives Congress.

Labarin mutuwar Aimola ya bayyana ne bayan da ya isa asibiti da aka kaishi a lokacin da ya sunbuke a kasa.

Naija News fahimta da cewa mamaicin ya bar Jam’iyyar APC ne a shekarar 2015 tare da Fasto Ize-Iyamu, a yayin da kuma yana cikin tsoffin membobin PDP da suka yi yunkurin komawa ga jam’iyyar su ta da ‘APC’ a yayin da ya fantsama a gidan Ize-Iyamu.

An bayyana da cewa a da ya kasance tsohon dan takaran Ciyaman ne na yankin Gabacin Owan, karamar Hukuma a Jihar Edo.

Wani tsohon Sakataren Gabacin Owan, Mista Godwin Imoudu, wanda ya tabbatar da rasuwarsa ya ce marigayi Aimola ya kasance ne a Benin don ficewa zuwa Jam’iyyar APC.