Connect with us

Labaran Najeriya

Sowore: Kungiyar Amnesty International ta zargi Shugaba Buhari da tsoratar da ‘Yan Najeriya

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Kungiyar Amnesty International a wata sanarwa ta zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da yin amfani da jami’an tsaro da kuma bangaren shari’a don tsananta wa ‘yan Najeriya.

Kungiyar yaki da haƙƙin ɗan Adam din ta bayyana hakan yayin da ta la’anci ci gaba da tsare jagoran ƙungiyar #RevolutionNow, Omoyele Sowore ta hannun ma’aikatar tsaro ta DSS.

Naija News ta ruwaito a Manyan Labaran Jaridun Najeriya a baya da cewa a Ma’aikatar hukumar tsaron kasa (DSS)  sun harba tiyagas da bindiga don tarwatsa masu zanga-zanga da suka afka wa ofishinta don neman sakin Omoyele Sowore.

Deji Adeyanju wanda ya jagoranci zanga-zangar tare da mabiyansa sun mamaye ofishin hukumar ne a Abuja domin neman a saki Sowore nan da nan.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa zanga-zangar tasu ya biyo ne sakamakon jinkirta da hukumar DSS ke yi ga sakin Sowore, bayan da kotun koli ta riga ta bayar da umarnin a sake shi tun kwanakin baya.