Uncategorized
An Kubutar da Yarinya Mai Shekaru 11 da Ake Ciyar da Ita da Kyankyasai da Bayi a Anambra
Haris Harrison, mai fafutukar kare hakkin Dan-Adam, ya samu nasarar ceton wata ‘yar yarinya mai shekaru 11 wanda maigidanta ya kulle a cikin kurkuku.
Bisa rahotannai, Naija News ta fahimci cewa maigidan kan bugi yarinyar sau da dama har ma da barin ta da mumunar raunuka ko ta ina a jikunanta. Abin takaici, har ma akan ciyar da ita da kyankyasai hade da bayi a kullum.
Karin rahotanni game da lamarin ya bayyana da cewa yarinyar a hakan tana karban magani a Asibitin Amaku da ke Awka.
Rahoton ya bayyana ne sa’adda Gwamnishu ya rubuta a kafafen sada zumunta cewa: “Wata Macce Ta Kulle ‘Yar Shekara 11 da haihuwa, Tana Ciyar da Ita da Kyankyasai hade da bayi, anan Akwa, babba birnin Jihar Anambra.”
“Wani mazauni da abin dama ya rahoto garemu da batun wata yarinya ‘yar shekaru 11 a gidan da aka kulle, da ake kuma yi wa duka bayan ciyar da ita da kyankyasai.”
“Da jin hakan, a cikin hanzari muka kama kai zuwa Awka don kubutar da yarinyar daga kurkuku inda aka dakile tare da raunuka ko ta ina a jikunanta. A Yanzu haka tana kwance a Asibitin Amaku, Awka, inda ake bata kulawa.”
Kalli Hotunanta a kasa;