Connect with us

Labaran Najeriya

Shugaba Buhari Yayi Rashin Biyayya ga Umarnin Kotun Koli 40 Tun daga 2015 – Lauya

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

An zargi Shugaba Muhammadu Buhari da gaza bin umarnin kotu a lokuta da dama tun bayan da ya zama shugaban Najeriya a shekarar 2015.

Kolawole Olaniyan, mai ba da shawara a fannin shari’a ga kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International, ya yi zargin cewa Shugaba Buhari ya nuna “rashin ladabi ga bin doka da take hakkin dan Adam, yin watsi da alƙalai na Najeriya a aƙalla sau 40 tun daga shekarar 2015 da ya hau karagar mulkin kasar.

Ka tuna kamar yadda Naija News Hausa ta ruwaito a baya cewa Wani jigo a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta reshen jihar Ebonyi, Charles Enya, ya shigar da kara wanda ke neman a yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima domin bai wa Shugaba Muhammadu Buhari damar tsayawa takara a karo na uku.

Enya, wanda ya kasance sakataren shirye shirye ga shugaba Buhari yayin babban zaben shekarar 2019, ya shigar da karar mai lamba (FHC/AI/CS/90/19) a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abakiliki, bisa rahoton da aka bayar a hannun jaridar Daily Trust.