Connect with us

Labaran Najeriya

Shekaru Na 9 A Makarantar Bodin Ya Canza Mini Rayuwa – Buhari

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00
Ranar Rantsar da Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari a ranar Litinin 2 ga Disamba, ya ba da labarin rayuwarsa tun yana dan saurayi da rayuwarsa a makarantan sakandiri. A wata sanarwa daga mai ba Shugaba Buhari shawarwari ta musamman kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, shugaban ya ce ya zama maraya ne tun yana dan karamin yaro.

A cikin bayanin kuwa, Shugaban ya kara da cewa shekaru tara da ya yi a makarantar Bodin (Watau Makarantar da Dalibai ke kwana a ciki) da kuma shiga Soja ya tsara rayuwarsa gaba daya.

Ya kuma ce tattalin arzikin Najeriya da ceton siyasar kasar zai zo ne daga samun Ilimi.

Da shugaban ke hidimar bikin tunawa da bikin cika shekaru 50 da kafa makarantar sakandare ta Daura, inda aka karrama shi, Shugaba Buhari ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su rungumi karantarwa a matsayin hanyar rayuwa yayin da gwamnati za ta yi iya bakin kokarin ta don bayar da daman hakan.

“Na yi tsawon shekaru tara a makarantar bokon da ake kwana, inda malamai suka tausaya mana da nuna kauna, kulawa da kuma jajircewa baki daya. Sun riƙe ku kamar ‘ya’yansu. Sukan kuma yaba mana lokacin da muka kokarta, kuma sukan buge mu a gefunan duwawunmu idan muka yi rashin ji,” inji Shugaba Buhari.

Ya kuma yaba wa hukumar da ke kula da gudanarwan makarantar, wacce a haka an sake wa lakabi “Pilot Secondary School, Daura, saboda kiyaye kyawawan halaye yayin da suke gargadin Kungiyar tsohin ‘yan makarantar a kan ci gaba da kyakkyawan aiki da suke yi kan makarantar.

KARANTA WANNAN KUMA: Majalisar Zartarwar Zamfara ta Soke Dokar Bayar Da Fansho Ga Tsoffin Gwamnonin, hadi da Wasu.