Labaran Najeriya
Shugaba Buhari da Uwargidansa, Aisha sun cika Shekara 30 da Aure (Kalli Hotuna)

Uwargidan Muhammadu Buhari, shugaban kasar Najeriya, Aisha Buhari a ranar Talata, 2 ga watan Disamba a shekara ta 2019 ta gabatar da murnanta da cikarsu shekaru 30 ga aure.
Sakon nata wanda ta aika a shafin nishadewa da sadarwa ta yanar gizo, Twitter, ta ce;
“Alhamdulillah ga cika shekaru 30 tare ga Aure.”
Ga sakon a kasa hadi da bidiyo kamar yadda Aisha ta watsar:
Alhamdulillah for 30yrs of togetherness .#30yearsweddinganniversary#ThanksbetoALLAH pic.twitter.com/gwAAJoHlkN
— Aisha M. Buhari (@aishambuhari) December 2, 2019