Labaran Najeriya
Gwamnan PDP Ya Bayyana Goyon Baya Ga Buhari Kan rufe Shingen Kasar
Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi, a ranar Litinin, ya ba da cikakken goyon bayansa ga matakin Shugaba Muhammadu Buhari na rufe iyakokin kasar.
Umahi ya bayyana matsayin sa ne kan zancen a yayin makon bude Babban Bankin Kasa, a filin wasa na Onueke da ke karamar Hukumar Ezza ta Kudu a jihar.
A cikin bayanin nasa, manufar rufe iyakar kasar za ta bunkasa tattalin arzikin manoma, da takaita kwararar makiyayan kasashen waje zuwa kasar tare da takaita haramtacciyar hanyar shiga da ficewar man fetur a kasar.
Umahi a yayin karin bayaninsa, ya ce;
“Ba za ku gane iyakan guba da lalaci da ake shigowa da ita a kasar nan da sunan shigo da shinkafar kasashen waje. Wannan rufe bakin iyakar kasar da shugaba Muhammadu Buhari ya dauka wani ci gaba ne, na amince da umarnin Shugaban kasa. A faɗi ko’ina.”
“Ebonyi ta kafa kai a haka cikin shirye-shiryen CBN. Na tsaya tare da Shugaban kasa game da rufe iyakar kasar. Za a taƙaita kwararar makiyaya masu kasashen mutane a Najeriya. Kan umarnin rufewar iyakar, manomanmu suna farin ciki.” inji Gwamnan.
Naija News Hausa ta ruwaito da cewa Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA ta Reshen Jihar Neja, ta kama wani mutum daya da ake zargi da daukar nauyin kilogiram 1,072 na Wiwi mai bugarwa a karamar hukumar Mokwa ta jihar.
Kwamandan NDLEA a jihar, Malama Sylvia Egwunwoke, ita ce ta sanar da hakan a cikin wata hira da ta yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya a Minna a ranar Asabar da ta gabata.