Connect with us

Uncategorized

Rikici A Yayin Da Wani Jami’in Tsaro Ya Harbe Wani Har Ga Mutuwa Yayin Bashi Tsoro

Published

on

at

advertisement

Rahoton da ke isa ga Naija News Hausa a wannan lokaci ya bayyana cewa wani jami’in ‘yan sanda ya harbe wani mai mota a wuyansa har ga mutuwa a wata unguwa a jihar Kano.

Bisa rahoton da jaridar The Nation ta bayar, an ce, mumunar abin ya faru ne ranar Laraba a tsohuwar birnin Kano, lokacin da wani jami’in ‘yan sanda, da ke hade da Bankin Kasuwanci, Bankin Stanbic, ya bude wuta ya kashe wani mutum, da aka bayyana sunansa da Mus’ab Sammani.

Abin ya faru ne a ofishin reshen bankin da ke kan titin Niger Avenue, a Mallam Kato Square, bangaren da ke fuskantar hanyar Post Office a shiyar.

A cewar wani da ya yi shaida da abin da ya afku, marigayin, Mus’ab Sammani da wani mai tukin Keke Napep sun shiga cikin wata muhawara ne mai zafin gaske, bayan da mai tukin Keke Napep din ya goga jikin motar sa.

Jaridar The Nation ta tattaro cewa jami’in da ake zargin, ya bar wurin tsaronsa ne don shiga tsakanin masu muhawarar mai zafi, saboda ya fahimci cewa gardamar tasu ta dauki zafi, za ta kuwa iya haifar da fada mai zafi. Anan ne ya umarci mai motar da ya janye motarsa ​​daga wurin zuwa wata bangare a kan hanyar.

An bayar da cewa yayin da marigayin yake kokarin yin biyayya ga umarnin jami’in, jami’in kuwa yayi tunanin cewa mamacin yana ƙoƙarin ya tsere ne yayin da ba zato ba tsammani ya jawo bindigarsa don ƙoƙarin yi masa barazanar.

Amma dai abin takaici, mai bada rahoto ya tattara cewa harsasan bindigarsa ta watse ta sami gilashin motarsa a gaba da kuma samunsa a wuya.

Kakakin rundunar ‘yan sanda, a yayin da ake zartawa da shi, DSP Abdullahi Haruna ya ce an garzaya da marigayin zuwa Asibitin koyarwa na Malam Aminu (AKTH), inda aka bada tabbacin mutuwar mai motar da ya mutu.

Haruna ya kara da cewa hukuma ta riga ta kama jami’in, kuma an fara bincike don gano abubuwan da suka faru da ya haifar da wannan mumunar lamarin.