Labaran Najeriya
Majalisar Wakilai Ta Tarayya Ta Zartar Da Kasafin Kudi Ta 2020
A yau Alhamis, 5 ga watan Disamba, Majalisar Wakilai ta Tarayya ta zartar da kudurin dokar kudi ta shekarar 2020, wanda ya karu daga jimillar kudi tiriliyan N10.33tn zuwa N10.6tn, fiye da yadda aka gabatar a da.
Wannan ya biyo bayan la’akari da zartawar rahoto da kwamitin majalisar suka bayar game da cancantar kudirin.
Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Kwamitin kula da kasafin kudi na majalisar ta gabatar da sabon adadi a yayin da ta gabatar da rahotonta game da kasafin kudin shekarar 2020 a ranar Laraba da ta wuce.
Kwamitin majalisar ta kuma ba da shawarar jimlar kasafin kudi na N10,594,362,364,830, fiye da yadda aka gabatar tun farko.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin farko ne tun ranar 8 ga Oktoba, 2019, inda ya gabatar da kudirin cancantar a zaman hadaka na majalisun dokokin kasar.