Connect with us

Uncategorized

Rundunar Sojojin Sama Ta Kadamar Da Operation Rattle Snake

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Rundunar Sojan Sama ta Najeriya, a karkashin rukunin yaki ta soja da aka fi sani da Operation LAFIYA DOLE, ta kaddamar da sabon rukunin mai taken “Operation Rattle Snake” don yaki da ta’addanci da ke gudana a yankin Arewa maso Gabas.

Air Commodore Ibikunle Daramola, Daraktan hulda da jama’a na hukumar NAF ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa a ranar Laraba da ta wuce a Abuja.

Daramola ya ce, rukunin sojojin saman wadda ta fara aiki a ranar Talata zata yi kokarin fuskantar wasu sashe a yankin Arewa Maso Gabas don nasara da ‘yan ta’addar da suka saura a yankin tare da hana su yaduwa da ‘yancin yaki.

Ya bayar da cewa a rana ta farko da rukunin sojojin suka tafiyar da ayyukansu, hakan ya haifar da nasara da fatattakar ‘yan ta’addar Boko Haram da rushe gine-ginensu a hedkwatar su na Parisu da kuma wani yankin zamansu a Garin Maloma, duka biyun a kusa da Sambisa.

Daramola ya ce NAF, wacce ke gudanar da ayyukanta tare da sojojin saman, za ta ci gaba da kokarinta na ganin ta lalata sauran ragowar ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa ‘Yan Bindiga Sun Sace Wani Darakta, Firinsifal da Dalibai 3 A Jihar Adamawa

Wasu ‘yan bindiga da ake zaton su da matsayin ‘yan garkuwa sun sace Daraktan ma’aikatar shari’ar jihar Adamawa, Barista Samuel Yaumande, da wani Firinsifal na Makarantar Sakandiri da wasu mutane 3 a Sangare, kusa da Jami’ar Fasaha ta Modibbo Adama (MAUTECH) a Yola.

A cewar wata majiya, ‘yan bindigar sun mamaye gidan Daraktan ne a daren Litinin din nan da ta gabata da misalin karfe 9:15 na yamma, dauke da muggan makamai suka fyauce da shi tare da makwabcin su wanda ke da matsayin firinsifal na wata makaranta tare da dalibai 3.