Connect with us

Uncategorized

APC/PDP: Atiku Da Asiwaju Tinubu Sun Hade A Jihar Neja

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar a ranar Asabar da ta gabata ya gana da tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu.

Ka tuna da cewa Atiku shi ne dan takarar shugaban kasa a babbar jam’iyyar adawa ta Najeriya, Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2019, a yayin da Tinubu shine shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Naija News ta fahimci cewa Tinubu ya hade da Atiku a Minna, babban birnin jihar Neja ne don karbar lambar girmamawa ta jami’ar Ibrahim Badamosi Babangida, Lapai.

Rahoton da aka bayar ga Naija News ya bayyana da cewa Gwamnan jihar Neja, Sani Bello, ya marabci Tinubu ne da mukarraban sa a lokacin da suka isa jihar don hidimar.

Haka kazalika gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya kasance mabiya bayan tsohon mataimakin shugaban kasan, Atiku.