Connect with us

Labaran Nishadi

Muna bada tabbacin tsaro ga zaben watan Fabrairun – Jami’an ‘Yan Sanda

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Sabon Kakakin yada yawun Jami’an tsaron ‘yan Sandan Najeriya, Frank Mba ya bada tabbaci ga ‘yan Najeriya da cewa jami’un su zata samar da kyakyawar shiri na tsaro ga zaben tarayya da ke gaba.

Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa IGP Mohammed Adamu ya umurci duk wadanda ke da bindigogi da makamai a gidan su da ba akan doka ba, su sadaukar da makaman ga jami’an tsaro kamin ya dauki mataki kan haka.

Jami’an tsaron sun gabatar da shirin su ne ta bakin kakakin jami’an, Frank Mba kamar yadda ya sanar a shafin nishadin jami’an a yau Laraba.

“Zamu tabbatar da cewa a karshen zaben shekara ta 2019 ‘yan sandan kasar Najeriya ta samu yabawa da gaske domin irin kokarin da zamu yi na samar da tsaro a lokacin zaben da ke gaba” in ij Frank.

Ko da shike wasu ‘yan Najeriya sun mayar da martani akan wannan bugun gaba da Jami’an tsaron suka yi na samar da tsaro ga zabe 2019.

Wani yace, shin dole ne sai lokacin zabe kamin ku bayana iya tsaro?

Wani kuma matashi ya zarge jami’an da cewa, shin kuna nufin sai kun sanya Buhari a mulki ke nan dai ko?

Bayanin na kamar haka: